Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Shirin Yarjejeniya Ta Duniya – Nijeriya.

 
 
Menene Yarjejeniya ta Duniya (Earth Charter)?

Zataswa ce game da manyan manufofi na al’umma,domin gina al’umman duniya amintacciya, jurarriya cike kuma da zaman lafiya a karni na 21. Tana da burin wayar da kan dukkan mutane,tana da kyawawan tunani game da dogara da juna da duniya ke yi,da hakoki domin cimma cigaban iyalin duniya,na al’umma masu rai baki daya da kuma na tsararraki masu zuwa.sa zuciya ce kan burin da ke gaba,kira ce kuma domin aiki.

Yarjejeniya Ta Duniyar ta fi bada hankali ne kan hanyar rayuwa jurarriya, ingantacciya kuma ga bil’adam. Daraja rayuwa a muhalli da na tsirrai ita ce mafi muhimmanci. Bugu da kari,Yarjejeniya Ta duniyar tana sane da manufofin kare rayuwa a muhali da na tsirrai,na kawar da talauci,tare da inganta tattalin arzikin mu domin kowa ya cimmoriyarsa,daraja ‘yancin bil’adam, demokuradiya,da kuma zaman lumana,wadannan sune ababan da ake dogarawa juna a kai,ba za a iya rarabewa ba. Yarjejeniyar tana tanada sabuwar hanyar cusa hadin kan al’umma wajen gudanar da aikin jagoranci mai jurewa na tsararraki nan gaba.

Yarjejeniya Ta Duniyar an yi ta ne don lokaci mai tsawo,a duniya baki daya,a tsakanin al’umomi,domin tattauna manufofi guda da dabi’unmu. An fara aikin Yarjejeniya Ta Duniyar ce  a matsayin wani shirin Majalisar Dinkin Duniya,daga bisani ne kungiyoyin al’umma a duniya suka dauka,suka kamala aikin. An kamala aiki kan Yarjejeniya Ta Duniyar ce a matsayin yarjejeniya al’umma a shekara ta 2000, lokacin da hukumar kula da Yarjejeniya Ta Duniya ta kadamas da ita,a matsayin yarjejeniya mai zaman kanta,tsakanin kasa da kasa.

Zana Yarjejeniya Ta Duniyar ta kunshi ani gagarumin hadin kai da aka taba samu,wannan hanyar da aka bi itace ginshiki babba na gina aiki mafi dacewa. An kuma sake karfafa amincewa da rubuttacen aikin ta wurin rattaba hannu da kungiyoyi sama da 4,500 suka yi, tare ma da gwamnatoci da kungiyoyi tsakanin kasa da kasa.

A game da amincewa da yarjejeniya da aka yi, lauyoyi da dama na kasa da kasa sun fahimci cewa Yarjejeniya Ta Duniya na da matsayi ne na karamar doka,kamar yadda dokar ‘yancin dan adam take,wanda ake kiyayewa a dabi’ance ba a shariance ba,domin bisa ga sharia ba dole ne wata gwamnatn kasa ta yi amfani da ita ba, sai dai kuma tana iya kasancewa wata hanyar samar da doka mai karfi ta fanin shari’a.

A lokacin da muke fuskantar manyan kalubai,na abinda muke tunani ko yadda muke zaman rayuwa,Yarjejeniya Ta Duniyar ta kan kalubalance mu,mu binciki dabi’unmu,mu kuma zabi hanyar da ta dacce. A lokacin da ake matukar bukatan abokan hulda, Yarjejeniya Ta Duniyar ta kan bada shawara yin aiki da manufa guda,duk da banbancin da ke tsakanin mu,mu kuma rungumi dabi’u na duniya,da mutane da dama a duniya ke cigaba da amincewa da su. A lokacin da ilimi ya kasance da matukar muhimminci wajen cimma nasarar raya cigaba mai ma’ana,Yarjejeniya Ta Duniya tana tanada matakan cimma burin ilimi mai jurewa.