Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Shirin Yarjejeniya Ta Duniya – Nijeriya.

 
 
YARJEJENIYA TA DUNIYA (The Earth Charter)

GABATARWA

Muna wani mawuyacin lokaci ne a tarihin duniya, lokacin da bil’adam zai zabi irin rayuwansa nan gaba. Yayin da Duniya ke cigaba da dogara ga juna a rashin karfi ko kumamanci, rayuwa nan gaba ta kunshi yanayi na masifa da alkawarai manya- manya. Kafin dai mu kai ga cigaba dolle ne, sai mun fahimci cewa a cikin al’adu da halin rayuwa daban-daban masu kayataswa; mu al’umman iyali guda ne na duniya da makoma guda. Kamata yayi kuma mu hada hannu wajen tabattar da jurewar al’umman duniya, wanda ke kafe kan ‘dabi’u na kwarai mai daraja halittu, daraja ’yancin biladama a duniya, ‘yancin tattalin arziki da kuma al’adar zaman lafiya. A dangane da haka ne, mu al’umman duniya muka furta hakkokin mu wa juna,domin rayuwan dukan al’umman duniya da kuma tsarraraki masu zuwa.

DUNIYA GIDANMU

Bil’adam na daga cikin halittun duniya.Duniya Gidanmu,na raye ne dangane da kasancewar rayyayun al’umma na gari da ke cikin ta. Halittun duniya masu karfi,sun sanya rayuwa cikinta ta kasance cike da bukatu da halin rashin sani. To amma duniya ta yi tanadin matakai masu muhimmanci ga rayuwa. Halin sake farfadowa daga duk wani hali na rayuwa da  al’umma ke da shi; da lafiyan bil’adam ya dangana ne kan tabbacin kiwon lafiya na kowane fannin rayuwa,da dukan ababan tarihi,tsire-tsire da dabbobi,kasar noma mai kyau,tsabtattaccen ruwa da kuma iska mai kyau. Karancin albarkatu a muhalin mu na duniya,shi ke ciwa al’umominta tuwo a kwarya. Amanar kare kyau, kuzari da bambace-bambancen da ke duniya shine sirin mu.

 YANAYIN DUNIYA

Halin tsarrafawa da yin amfani da abin da aka tsarrafa, kan janyo tabarbarewan muhali, rarrabe albarkatu,da yawan bacewan ire-iren halittu. Yin hakan kan kawo kaskanci ga al’umma. Babu rabo dai-dai.na albakar raya kasa, babban gibin nan da ke tsakanin ma azurta da matalauta sai kara buduwa yake yi. Rashin gaskiya a fanin shari’a,talauci,rashin sani da hargitsi wanda ya zama ruwan dare gama duniya,su suka zama sanadiyan wahaloin da ake fuskanta. Karuwan yawan jama’a a duniya, ya nawaitawa halin rayuwan al’umma da na ittatuwa. Akawai barazana kan tushen tsaro a duniya. Wadannan halaye na da hatsari, to amma ba abu ne da babu magani ba.

KALUBALAI DA KE GABA

Zabi ya rage garemu; ko mu hada kai don kulawa da duniyarmu da kuma juna, ko kuma mu fada cikin hasarar halaka kanmu da rayuwa daban-daban. Muna bukatan sauyi sosai a fanin dabi’u,matsayin mu da kuma halin rayuwanmu. Dole ne kuma mu fahimci cewa,matukar idan aka sami biyan muhimman bukatu;rayuwan bil’adam na raya cigaba shine na karuwa,ba na samu ba. Muna da ilimin da kuma fasahan tanada wa kowa, mu kuma rage hatsarin da muke da shi kan muhali. Hadin kan al’umma duniya da ya billo, ya tada sabbin dama da ake da su, wajen gina  demokuradiya da halin tausayi a duniya. Kalubalan da muke fuskanta a fanin muhali,tattalin arziki,siyasa,raya jin dadi da na ruhaniya suna nan iri daya,za mu kuma iya samun cigaba wajen magance su.

HAKIN MU NA DUNIYA

Kafin mu cimma nasarar burorinimu,dole sai mun fara sanya tunanin hakin mu na duniya a rayuwanmu. Mu fahimci kasancewan mu cikin al’umman duniya baki daya,tare ma da na kananan al’ummomi. Mun kasance al’umman daban-daban a duniya guda,inda kuma muka kasance daya a kananan matakai har zuwa matakin duniya baki daya.Kowa kuwa yana kulawa da hakin dan’uwansa domin rayuwa na gari wa iyalin bil’adam da na rayayyun halitu,a yanzu da nan gaba. Hakan zai karfafa rayuwa matuka, idan akwai hadinkai na bil’adam da dangantaka da ke tsakanin su, idan aka yi rayuwa domin girmama al’ajibin kasancewa a raye,mu kuma kasance da godiya domin kyauta rai,da kuma kaskanci samun kanmu a halittan duniya.

Muna matukar bukatan hangan gaba game da manyan dabi’unmu,da zumar gina harsashe mai kyau domin al’umman duniya mai tasowa. A dangane da haka,muke tabbatar da wadannan manufofi da ke da dangantaka da juna bisa sa zuciyar cewa, za a samar da hanyar rayuwa mai jurewa,bisa sayyayen mataki guda inda halin tafiyar da rayuwa na kowane mutum,da na kungiyoyi,wuraren kasuwanci,gwamnatoci da kuma na kungiyoyi  da ke aiki tsakanin kasa da kasa,domin a kiyaye a kuma same shi.

KA’IDODI

I. DARAJAWA DA KULAWA DA RAYUWAN AL’UMMA

1. Daraja duniya da rayuwa a fanoni daban-daban

 1. Kamata yayi mu san cewa dukan Bil’adam suna dogara ne ga juna,duk wani abu mai rai kuwa yana da daraja ko da  yaya dan adam ya dauke shi
 2. Kamata yayi a yi imani da irin darajar da ‘yan adam ke da shi,da ilimi a fanin iya zane-zane bin tsari da kuma yanayin sa a ruhu.

2. Kulawa da rayuwan al’umma tare da fahimta, tausayi da kauna

  1. kamata yayi a amince da ‘yancin malaka,tafiyarwa,da  amfani da albarkatun kasa,wanda ke tattare da hakkin kare illa ga muhalli da kuma ‘yancin mutane.
  2. Kamata yayi  a san cewa,yawan ‘yanci da ke karuwa,ilimi da karfi suna zuwa ne da karin sanin kokarin daukaka su don jin  dadin duka.

3. Gina al’umman demokuradiya mai gaskiya, mai tafiya tare,mai jurewa,kuma cikin lumana.

 1. a.  Kamata yayi a tabbatar da cewa al’ummomi a kowane mataki na kulawa da ‘yancin ‘dan adam a kuma baiwa kowa cikakken damar sanin irin baiwan da yake da shi.
 2. Kamata yayi a karfafa gaskiya a fannin raya jin dadi,da tattalin arziki,domin baiwa kowa damar neman hanyoyi tattali mai ma’ana domin tafiyar da rayuwa da ke da hakin kulawa da muhalli.

4. A kare yalwa da kyan duniya domin sararaki na yanzu da kuma masu zuwa.

 1. kamata yayi a san cewa ‘yancin aikatawa na kowace sara ya dangane kan bukatun sararaki masu zuwa.
 2. Kamata yayi a mikawa sararaki na gaba dabi’u,al’adu,da kuma manyan manufofi da ke goyon bayan cigaban’yan adam a duniya na lokaci mai tsawo tare da halittu da tsarrai da ke kewaye.

Domin a cimma nasarar wadannan manyan manufofi guda hudu,ya zama wajibi a:

II. DARAJA MUHALI MAI HALITTU DA TSIRRAI

5. Kamata yayi a kare a kuma sake farfado da darajar tsari na dangantakan halittu da tsirrai  a muhalin su, tare da yin la’akari da banbancin da ke tsakaninsu da kuma tsayayun hanyoyin tafiyar da rayuwa.

 1. Kamata yayi a rungumi shirye-shiryen raya muhalli da ka’idodi masu jurewa don kare shi, ya kuma kasance muhimmi a shirin raya kasa.
 2. Kamata yayi a kafa a kuma tsare kebabbun gandun daji da halittun da ke cikin ruwa,domin kare rayuwa na duniya,a karfafa kebe halittu,domin kare kasarmu na gado
 3. Kamata yayi a karfafa sake farfado da halittu da ke cikin hatsarin bacewa a doron kasa,tare da wadanda ke cikin ruwa.
 4. Kamata yayi a sanya ka’idadomin a shafe duk wani abu cikin halittu masu cutarwa.
 5. Kamata yayi a yi amfani da albarkatu masu iya sake hayayyafa kaman ruwa,kasa,amfanin da ake samu daga daji,da kuma halittun cikin ruwa,bisa hanyar da ba zai wuce gona da iri ba,har ya hana sake yaduwansu,domin kare lafiyansu.
 6. Kamata yayi a yi amfani da albarkatu wadanda basa sake hayayyafa kamar mu’adinai,ko matattun itatuwa,a bisa hanyar da zai rake hasarar su, da hatsarin bata muhali.

6. Kare hatsari a bisa mataki mafi dacewa wajen kare muhali,idan ko akwai karancin ilimi,sai a dauki matakin karewa daga aukuwa.

 1. Kamata yayi a tashi tsaye wajen hanna cutar da muhali sosai,wanda zai kai matsayin da ba za a iya magancewa ba,ko da ilimin kimiya kan hakan ba a kamala ba.
 2. Kamata yayi a dora laifin cutar da muhali kan wadanda ke musun cewa ayukan kimiya ba zai cutar da muhali  ainun ba.
 3. Kamata yayi a tabbatar da cewa shawarwari da ake daukawa,suna da la’akari da sakamakon su ga ayukan bil’adam a duniya baki daya,na lokaci mai tsawo,wuri mai nisa a fadin duniya baki daya.
 4. Kamata yayi a kare muhali daga dukan wani irin datti mai guba,a kuma hanna gina sinadarai masu guba kan muhali.
 5. Kamata yayi a guji ayuka irin na sojoji da ka iya cutar da muhalli

7. A amince kan hanyoyin tsarafawa, yin amfani da abin da aka tsarafa, wanda zai kare halin sake hayayafa na duniya,bisa ‘yanci ‘yan adam da lafiyan al’umma.

 1. Kamata yayi a rage,a sake amfani, a kuma sake tsarafa kayyakin da aka yi amfani da su, akuma tabbatar da ganin abin da suka ragu,zasu kasance da amfani ga rayuwan hallitu da tsirrai.
 2. Kamata yayi a yi sannu a hankali,bisa amfani da karfin wuta,a kuma kara dogara ga hanyoyin samar da karfin wuta masu jurewa kamar hasken rana da kuma iska.
 3. A karfafa raya kimiya da suka shafi muhali,a amince da su,a rarraba su dai-dai wa kowa.
 4. A tabbatar da farashin kayayyaki da ayuka a yadda ya shafi muhalli da raya jin dadi ya kasance a gida,a kuma kyale masu amfani da kayayyakin su gano ko wanene mafi dacewa da bukatun su na muhali da raya jin dadin su.
 5. A tabbatar kowa ya iya kaiwa ga samun cikakken kiwon lafiya,domin inganta kiwon lafiyar haihuwa ta kowace fanni.
 6. Kamata yayi a rungumi halin rayuwa da ke bada karfi kan darajar rayuwa da isasun kayayyaki a duniya mai shudewa.

8. A inganta nazari wajen karfafa rayuwan hallitu da tsirrai, a kuma karfafa yin amfani da kuma musanyan ilimin da aka samu.

 1. Kamata yayi a goyi bayan kimiya da fasaha na kasa da kasa kan tabbatar da jurewan ababa, a kuma bada hankali musamman kan kasashe masu tasowa.
 2. Kamata yayi a fahimci  a kuma kare ilimi gargajiya da ikima ko basira na ruhu,a dukan al’adu wadanda ke taimakawa wajen kare muhali da lafiyar ‘dan adam.
 3. A tabbatar an iya samun bayyanai da sadarwa a fili,masu muhimmanci wa kiwon lafiyan ‘dan adam da kuma muhali har ma da abin da ke jini.

YIN GASKIYA A FANIN RAYA JIN DADI DA TATTALIN ARZIKI.

9. Kawar da talauci,a matsayin matakin gaggawa don yin abin da ke dai-dai,don raya jin dadi da muhali.

 1. Kamata yayi a tabbatar da ‘yancin samun sabtattaccen ruwa,iska,da abinci,da doron kasa maras guba,matsuguni,da tsabtar muhali,tare da yin amfani da albarkatu na kasa da kuma tsakanin kasa da kasa,wadanda aka amince da su.
 2. Kamata yayi a tanada  ilimi wa dukan’yan adam,da albarkatu na tsare rayuwa,da na raya jin dadi da kuma hanyoyin taimakawa wadanda ba za su iya taimakon kansu ba.
 3. Kamata yayi a san da wadanda aka yi watsi da su,a kare wadanda ka iya faduwa cikin hatsari na rayuwa,a taimakawa masu wahala,a kuma basu zarafin  aiwatar da burinsu na rayuwa.

10. Tabbatar da ganin ayukan tattalin arziki da manyan kungiyoyi a kowane mataki sun bunkasa cigaban bil’adam a hanyoyin da ke dai-dai mai jurewa kuma.

 1. kamata yayi a karfafa batun rarraba arzikin kasa ta fanin ilimi,kudade,fasaha da kuma jin dadin al’umma,a kuma rage yawan basusuka daga waje da kasashen masu tasowa ke da shi.
 2. A tabbatar an yi amfani da sahihan hanyoyi,na goyon baya ta fuskar kasuwanci,yin amfani da albarkatu,kare muhalli da kuma ayukan kodago.

11. A karfafa wajen haramta banbancin jintsi sinadarin samar da raya kasa mai jurewa,a kuma tabbatar da samar da ilimi wa kowa ,tare da kiwon lafiya,da kuma tattalin arziki.

 1. A kare hakki mata da yara mata,a kuma haramta musguna masu.
 2. A karfafa kasancewan mata cikin ayukan siyasa, tattalin arziki,raya cigaba,da na al’adu a matsayin masu ‘yanci iri guda,a fanin daukan shawarwari, shugabanci da cimmoriya.
 3. A karfafa iyalai akuma tabbatar da kare lafiya da kaunar kowane gaa cikin iyalin.

12. A karfafa yancin kowa ba tare da wariya kan muhallin da jin dadin al’umma mai goyon bayan darajar bil’adam,kiwon lafiyansa da rayuwansa ta addini,a kuma bada hankali musamman kan ‘yancin alumman karkara da marasa rinjaye.

 1. A kawar da nuna wariya ta kowace hanya,wala ta kabila,launi,jintsi,yanayin sanin jima’I,addini,kabila,kasa,al’umma ko raya jin dadi.
 2. A tabbatar da ‘yancin al’umman karkara kan harkokinsu na addini,ilimi,dogaro da kai,albarkatu,da kuma rayuwansu na yau da kullum.
 3. A girmama a kuma goyi bayan matasa cikin al’ummomin mu,a basu damar cika burinsu,wajen kirkiro al’ummomi masu jurewa.
 4. A kare a kuma maido da wuraren tarihi da na gargajiya dangane da muhimmancin da suke da shi a rayuwar addini.

IV. DEMOKURADIYA,BABU HATSARI,CIKIN LUMANA.

13. A karfafa kungiyoyin deokuradiya a kowane mataki, a samar da mulkin gaskiya,mai  iya bada lissafi,mai karban shawara,a kuma tabbatar da shariar gaskiya.

 1. A tabbatar da ‘yancin kowa a fanin samun bayyanai filla-filla,kuma kan lokaci game da abin da ya shafi muhalli,da kuma dukkan shirin inganta kasa,da duk wani aikin da ya shafe su ko suna da ra’a yi a kai.
 2. A koy bayan al’ummomi na kananan hukumomi,na shiyoyi,da na duniya baki daya,a kuma karfafa duk mai sha’awa ko kungiyoyi su bada kai wajen bada shawarwari.
 3. A kare ‘yancin fadin ra’ayi furuci,taruka cikin lumana,kungiyoyi da mazaunin mutum na asali.
 4. A karfafa hanyoyi masu sauki wajen samun ‘yanci a harkokin shari’a,da samar da hanyoyin magance su,a kuma sake yin la’akari da illar da ake yi wa muhalli,da irin barazanar da yin hakan ka iya janyowa.
 5. A kawar da almubazaranci a dukkan mataki na kungiyoyi masu zaman kansu ko na al’umma.
 6. A karfafa al’momin karkara, domin basu damar kulawa da muhallinsu,a kuma sanya hakkin kulawa da muhali kan gwamnati a dukkan mataki,domin iya tafiyar da su kamar yadda ya kamata.

14. A cusa ra’ayin ilimi bisa daraja da iya aiki da ake bukata na rayuwa cikin munhajan ilimi na zamani.

 1. A tanadawa yara da matasa musamman,damar samun ilimi da zai karfafa su wajen tofa albarkacin bakinsu kan inganta kasa.
 2. A karfafa aikin zane da na bil’adam da kimiya da zumar samar da ilimi mai jurewa.
 3. A inganta matsayin kafofi watsa labarai da zumar wayar da kan al’umma game da kalubalai da ke tasowa a fanin tsirrai da muhalli da kuma raya jindadi.
 4. A fahimmci muhimmancin dabi’un kwarai da na addini wajen tabbatar da rayuwa na gari.

15. Kamata yayi a dauki kowane mai rai da daraja tare da kula.

 1. A hana wulakanta dabbobin da ke zaune cikin al’umma,a kuma kare su dga shan wuya.
 2. A kare dabbobi masu hatsari daga hannun mafarauta,da masu kama kifaye don kare su daga bacewa da wahala.
 3. A guji ko a kawar da karba ko halaka hallitu da ba a nufesu da hallakawa ba.

16. A raya al’adar yin hakuri da juna,ba hargitsi,cikin lumana.

 1. A karfafa a kuma goyi bayan fahimtar da juna,nuna goyon baya da hadin kai ga dukkan al’umma kuma tsakanin kasashe.
 2. A samar da matakai masu karfi wajen hanna barkewar hargitsi, a hada kai wajen magance matsaloli da suka shafi muhali da dai sauran rigingimu da ka iya tashi.
 3. A guji yin amfani da karfin soja a fanin tsaro,ya zuwa wani matsayi na rashin jin cakuna,har ya kai matakin da za a yi amfani da kudade da aka kiyasta na tsaro,a hanyoyin samar da zaman lafiya,ciki ma har da farfado da raya yanayin muhali da n tsirrai.
 4. A kawar da makaman nukiliya da masu guba,da sauran makamai irin na kare dangi.
 5. A tabbatar cewa amfani da ake yi da duniyar gizo,da kayayyakin kimiya da ake harbawa sararin sama,suna goyon bayan kare muhali ne da zaman lumana.
 6. A fahinci cewa zaman lumana ya kunshi dukkan komai,da ke haifar da dangantaka na kwarai,na wasu mutane, na al’adu,na wata rayuwa dabam,na duniya,da na duka,inda kowa ke kunshe cikin ta.

HANYAR CIGABA

Abin da ba a taba samu ba a tarihin duniya, kasancear mu da makoma guda ya zuga mu wajen neman sake komai. Yin hakan na kushe ne cikin al’kawaran da ke cikin wannan Yarjejeniya Ta Duniya. Kafin ko mu cimma nasarar cika al’kawaran nan, sai mun mika kanmu domin mu amince mu kuma raya,dabi’u da manufofin wannan matsayi da duniya ta dauka.

Hakan ko na bukatar sauyi na tunani,da na zuciya. Yana bukatar sabon tunani game da dogara da duniya kewa juna,da halin sanin ya kamata. Dole ne muyi tunanin rayuwa da kuma amfani da burin nan,ta hanyar tafiyar da rayuwa a matakin karkara,kasa,shiyya,da na duniya. Al’adun mu daban-daban gado ne na musamman. Al’adun nan za su samar da hanyoyi,wajen cimma burin nan. Dole ne kuwa mu zurfafa mu kuma fadada tattaunawa na duniya,wanda ya haifar da Yarjejeniya Ta Duniya,domin ko muna da abin koyi sosai,kan wannan binciken hadin gwiwa da ake yi,da nufin cimma gaskiya da hikima.

Rayuwa dai tana kunshe ne da fargaba,a tsakiyan dabi’u masu muhimmancin gaske. Ma’ana, za a iya cimma mawuyacin yanayi na yin zabi. To amma dole mu nemi hanyoyin hada kan banbance-banbancen mu,a kuma yi amfani da ‘yancidomin cimmoriyar duka,da manufofi na kankanin lokaci,da na lokaci mai tsawo. Kowane mutum,Iyali,kungiya da al’umma na da muhimmin rawa da zai taka. Ana kira ga masu kimiya na zane,addini,kafofin ilimi,kungiyoyin da ba na gwamnati ba,tare ma da gwamnatoci, da su gudanar da shugabanci na gari. Hadin kan gwamnati da kuma al’umma da na ‘yan kasuwa na da muhimmanci wajen samar da gwamnati na gari.

Idan ana bukatan gina al’umman duniya mai jurewa,dole ne kasashen duniya su sake sabunta mika kai ga majalisar dinkin duniya,wajen bin tsarin dokokinta,karkashin yarjejeniya ta kasa da kasa,a kuma goyi bayan aiwatar da manufofin Yarjejeniya Ta Duniya,da ke da hurumi kan raya muhalli.

Bari wannan lokaci ya kasance wanda zamu rika tunawa da batun farfado da sabuwar hanyar girmama rayuwa, mu kuma kudurta cimma nasarar burorinmu masu jurewa tare da karfafa gaggauta gwagwarmayar samar da gaskiya a fanin sharia da zaman lumana da farincikin kasancewa a raye.