Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Shirin Yarjejeniya Ta Duniya – Nijeriya.

 
 
TSARIN ECI DA WURAREN BADA HANKALI:

Wadannan sune manufofi na musamman kan shirin Yarjejeniya Ta Duniya:

  1. Ta wayar da kan jama’a a duniya baki daya game da Yarjejeniya Ta Duniya,ta kuma karfafa fahimta game da manufarta na cusa dabi’u.
  2. Ta nemi a san da ita a kuma amince da Yarjejeniya Ta Duniya,tsakanin mutane,kungiyoyi da kuma majalisar dinkin duniya.
  3. Ta karfafa amfani da Yarjejeniya Ta Duniya a matsayin jagora kan dabi’u, ta kuma aiwatar da manufofinta tsakanin alumomi, ‘yan kasuwa, da gwamnatoci.
  4. Ta karfafa ta kuma sami goyon bayan yin amfani da Yarjejeniya Ta Duniya a fagen ilimi, kamar makarantu, Jami’o’I,kungiyoyin addinai,alu’momin karkara.
  5. Ta karfafa sanin Yarjejeniyar a kuma yi amfani da ita a matsayin karamar doka.

TSARE-TSARE GAME DA BADA IKON HANA CINKOSO:

‘Bada ikon hana cinkoso domin kusawa gaba’ shine sunan da aka baiwa tsare-tsare da shawarwari da aka dauka a shekara ta 2007. Manufar wannan tsarin shine domin a karfafa  fadada shirin Yarjejeniya Ta Duniya, ba tare da fadada cibiyar gudanarwa kawai ba. Ta kuma bada izinin samar da kokarin fadada aikin, ta hanyoyi da dama na kai da kai.

Bisa goyon bayan wannan sabon tsarin ne kuwa, aka kafa matakan tafiyar da ikon hana cinkoso na shirin Yarjejeniya Ta Duniya. Idan aka yi amfani da wannan matakan kowane mutum, ko kungiya, ko al’umma, za su iya amfani da Yarjejeniya Ta Duniya a bisa hanyoyin da suka dace da irin damar da ake da shi.

WURAREN BADA HANKALI DA HUKUMOMIN KARFAFA DOKA:

A taron ta na uku na shekara-shekara, a watan Mayu shekara ta 2008, Majalisar Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa(ECI) ta amince da kafa hukumomin karfafa Doka guda shidda(6),a bisa shiri na tsawon lokaci, da ke kafe kan tsare-tsare na ikon hana cinkoso wuri guda,wanda kuma aka zana domin ya hanzarta fadada ayukan Yarjejeniya Ta Duniya a ko’ina. Kowace hukumar karfafa doka zata bada karfi kan raya dangantaka da karfafa ayuka a daya daga cikin wadannan hanyoyi:

- Kasuwanci
- Ilimi
- Kafofin watsa labaru
- Addinai
- Majalisar Dinkin Duniya
- Matasa

An zabi wadannan fannoni shidda ne, domin suna tanada muhimmin dama wajen yin amfani da Yarjejeniya Ta Duniya don sauyi ya zuwa hanyoyin rayawa mafi dacewa. A yawancin wadannan fannoni shidda,an riga an fara ayuka da dama, wanda zai baiwa hukumomin karfafa doka damar gini a bisan sa. A dukan wadannan fannoni, akwai damar samun yaduwa kamar wutan daji, na sha’awar Yarjejeniya Ta Duniya, fiye da yadda aikin hukumar karfafa doka ta yi tun farko.

An tsara hukumomin karfafa doka ne domin, su yi aiki a matsayin masu mika kai,da zai kai ga samar da shirye-shirye masu zaman kansu. Majlisar ECI ce ta yi tunanin sa, wanda kuma membobin Majalisar ECI dabam-dabam masu aiki a matsayin wani ayari na “SEED” suka kaddamas. Babban komitin majalisar zattaswa ce take amincewa da zaben shugabanin ayarin na dukan hukumomin karfafa doka. Itace kuma ke da hakkin duba cigaban ayuka na kowace hukumar karfafa doka, lokaci-lokaci. Duk da haka, Majalisar ECI da Sakatariyar ECI ba za su bada umurni ko su taiyar ECI ba za su bada umurni ko su tafiyar da aiki na hukumomin karfafa doka ba. Sakatariya zata tanada muhimman ayuka domin marawa hukumomin karfafa doka baya. Sakatariyar har ila yau, zata iya gudanar da wasu ayuka na daukaka aikin wasu hukumomin karfafa doka, matukar tana da kwarewa a fanin; tana kuma ababan taimakawa, misali, a fanin ilimi. Ana sa ran cewa ayarin shugabanin hukumomin karfafa doka, za su kunshi mutane da dama, wadanda ba membobin majalisar ECI ba ne. wasu kungiyoyi kuma za su iya tanada ayuka wa hukumomin karfafa doka, hakan zai bada hanga mai fa’di game da sakatariyar.

Dalilin kirkiro da shirin bada iko kan tsare-tsaren hana cinkoso, da kuma kafa hukumomin karfafa Doka,ya danganta ne kan tabbatacin cewa shirin Yarjejeniya Ta Duniya na dangantaka ne,amma ba na kungiyar da ba ta gwamnati ba(NGO). Ba shi yiwuwa shirin Yarjejeniya Ta Duniya ta fadada kwarjinin da take da shi a duniya baki daya,ta kuma cimma burinta, matukar ana ganin ta a matsayin kungiyar da sakatariyar ECI ke jagorancin ta kawai. Idan aka yi la’akari da manufar Yarjejeniya Ta Duniya, ba zai iya yiwuwa a ce wata kungiya babba mai zaman kanta ce ke sa ido kan ayukanta a duniya baki daya ba. Kuma sakamakon yin hakan zai kasance da mamaki. Aiki ne da ba zai taba yiwuwa ba, ba kuma hikima cikinsa.

A kashin gaskiya shirin Yarjejeniya Ta Duniya ya yadu hannun dubban mutane, da kungiyoyi wadanda yawancin lokaci suna hada kai ne, ba sa yawan aiki a kadaice ba. Majalisar ECI ce ke billo da manufofi da tsare-tsare wa sakatariyar ECI, wadannan manufofi da tsare-tsare ne suke zama jagora ga kowane fani na Yarjejeniyar. Karamar sakatariyar na gudanar da muhimman ayuka kalilan; kamar shugabancin Yanar gizo ta kasa da kasa, da kuma shirya wasu muhimman kayan aiki. Yawancin ofisoshin membobin majalisar ECI, suna bada goyon bayan su wa sakatariyar a yankuna dabam-dabam a duniya.

Shugabancin kowace hukumar karfafa doka, zata kasance ayari ne,na akalla mutane biyu zuwa goma. Manufar kowace hukumar karfafa doka ita ce zuga sabbin ayukan Yarjejeniya Ta Duniya, ta kuma daukaka batun fadada  ayukan Yarjejeniyar. Kowace hukumar karfafa doka, zata fara aikinta,tana neman sanin bambanci muhimmi da ayukan Yarjejeniyar ke yi a yankinsa, da kuma fahimtar irin gibin da Yarjejeniyar zata iya cikawa zai kuma kasance wajibi a billo da wani shirin aiki na gajere da kuma  na tsawon lokaci, da kuma bin tsarin da zai cimma wadannan munufofi.

Hukumar karfafa dokar zata lisafta shugabani masu mika kai, da kuma goyon baya da ake bukata wajen aiwatar da shirye-shiren. Dole ne kuma ta yi tattalin muhimman ababan da ake bukata. Kowace hukumar karfafa doka zata yi zaman kanta a fanin hada kan jakadu da masu zurfafan ra’ayi game da Yarjejeniya Ta Duniya.

A bisa shiri na lokaci mai tsawo, majalisar ECI ta amince har ila yau, da ayuka guda biyu, da suka shafi kara kaimi wa aikin yanar gizo da ke gudana a duniya baki daya.  A halin yanzu; shirin Yarjejeniya Ta Duniya da shirin kayayakin sadarwa, da suka hada da littattafai,da littafin bayanai, da  majigi da ake bukata domin goyon bayan fadada shirin a wuraren da hukumomin karfafa doka suka fi bada kai. Yanar gizo na duniya baki daya, zai kunshi kirkiro ta a kowace kasa,kuma a harsuna da suka cancanta. Dukkan wadannan za su kasance dalabarai da bayyanai iri guda; game da Yarjejeniya Ta Duniya, da shirinta za a iya sake tsarafa shi domin ya cimma manufa na karkara. Sakatariya zata taimaka da ayukan nan biyu.

Sakatariya zata tura rahotani lokaci-lokaci game da Yarjejeniya Ta Duniya a yanar kizo game da ayukan hukumar karfafa doka,da kuma kan yanayin cigaba da aka cimma game da ayukan nan biyu.
Duk mai sha’awar goyon bayan hukumar karfafa doka, ana karfafa su, su tuntubi ayarin shugabanin kai tsaye.