- Ka yada labarin Yarjejeniya Ta Duniyar, da kuma wayar da kai game da ita tsakanin abokan ka da al’umanka.
- Ka amince da Yarjejeniya Ta Duniya, ka kuma karfafa kungiyoyi da kake ciki, tare ma da gwamnati kananan hukumomi da na kasashe da su yi amfani su kuma amince da ita.
- Ka fara wata kungiyar nazari kan Yarjejeniya Ta duniya,ka kuma binciki yadda za a yi amfani da manufofin Yarjejeniya Ta Duniya a gidaje,wurin aiki, da amfani cikin alu’mma.
- Ka hada hannu cikin shirin Yarjejeniya Ta Duniya karkashin hukumar karfafa doka wanda ke aiki a fanoni guda shida(6):- ilimi, kasuwanci,kafa watsa labarai, matasa da majalisar dinkin duniya.
- Ka hada kai da abokan hulda na Yarjejeniya Ta Duniya, tare ma da sauran kungiyoyi da suka amince da Yarjejeniyar a yankin ka.
- Ka tanada taimako na kudi ko ka tanada wasu kayayyaki, ko aiki da ake bukata wajen goyon bayan Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa, da sauran ayuka na Yarjejeniya Ta Duniyar.
- Ka tuntubi, ka kuma Bi tsarin gudanarwa kan fadada aiki ta wurin hana cinkoso na shirin Yarjejeniya Ta Duniya, wanda za a iya samu a yanar gizo na Yarjejeniya Ta Duniya.
Akwai hanyoyin amfani da Yarjejeniya Ta Duniya da dama, kamar a makarantu,wuraren kasuwanci, gwamnatoci, kunyoyin da ba na gwamnati ba, taruruka, da sauran taro na jama’a. Ga misali, za’a iya amfani da ita a matsayin:
- Munhajan ilimi, wajen samar da fahimtarwa game da manyan kalubalai, da zabi da ke fuskanra bil adam, da kuma manufar samar da rayuwa mai ma’ana.
- Kira domin aiki, kuma jagora kan dabi’u don samar da rayuwa mai ma’ana da zai karfafa bada kai, hadin kai da sauyi na gari.
- Muhimmin jagoranci wa gwamnatoci a kowane mataki, bisa tsarin manufofin su, da zummar gina al’umma na gari, a kuma samar da zaman lafiya mai jurewa a duniya.
- Muhimmin aiki, wajen jan hankali kan hakokinmu na kulawa da rayuwa da tsirrai da muhalinmu. A kuma billo da muhimman sadarwa da za’a yi amfani da su.
- Sinadarin ingiza tattaunawa tsakanin sassa, da aladu, tsakanin addinai game da manufofi guda, da ake da su.
- Karamar doka,da ya kasance tushen dabi’u, na irin cigaba da ke gudana a muhali, don cimma yunkurin raya doka mai jurewa.
- Na;urar auna cigaba, don kaiwa ga jurarriyar rayuwa.