Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Shirin Yarjejeniya Ta Duniya – Nijeriya.

 
 
Takaitaccen Tarihi Game Da Shirin Yarjejeniya Ta Duniya (Earth Charter)

Yarjejeniye Ta Duniya zattaswa ce ta mutane kan dogara da juna da duniya ke yi. Hakki ne na Duniya wanda ke billo da tsare –tsare game da gina Duniya amintacciya,jurarriya, cike da zaman lumana. Ta dukupa wajen gano manyan kalubalai na yin zabe, da ke fuskantar ‘yan adam a karni na Ashirin da daya(21). An zana tsare-tsaren ta domin ta cimma matsaya guda; idan za a jagoranci a kuma auna halayen kowane mutum guda, kungiyoyi,’yan kasuwa, gwamnatoci,da majalisun gargajiya(Gabatarwa ta Yarjejeniya Ta Duniya) Yarjejeniya Ta Duniya shiri ne da aka yi a lokaci mai tsawo, na duniya baki daya,tsakanin al’adu dabam-dabam, da aka tattauna game da manuffi guda, da dabi’u iri guda,da ya gudana cikin shekara ta 1990.  Wannan matakin da aka dauka ya kunshihada kan mashawarta mafi yawa da aka taba samu,a game da wani shiri na kasa da kasa, shine tushen farko game da amincewar da aka yi da Yarjejeniya Ta Duniya a matsayin tsarin doka.

I. Tushen Yarejeniya Ta Duniya

Daga cikin shawarwari da ke cikin RAYUWARMU GUDA NAN GABA(1987),rahoton hukumar kula da muhali da raya kasa(WCED)kira ce ta kirkiro da zattaswar duniya game da kare muhalli da raya kasa mai jurewa,a cikin sabon mazubi na Yarjejeniyar,dauke da tsare-tsare na jagorancin kasashe har ya zuwa ga raya kasa mai jurewa. Da yake kara gini kan shawarwarin  nan, Maurice F. Strong, babban sakatari a taron Koli na Duniya da ya gudana a Rio, a shekara ta 1992 ( Taron majalisar Dinkin Duniya kan muhali da raya kasa), ya bada shawara a shekara ta 1990 cewa kamata yayi taron koli ta zana ta kuma rungumi yarjejemiya Ta Duniya. An gudanar da taruka na mashawarta tsakanin gwamnatoci game da wannan Yarjejeniya Ta Duniya lokaci shirye-shiryen taron koli na Rio, to amma an kasacimma amincewa kan tsare-tsare na Yarjejeniyar. Zattaswa ta Rio wadda aka gabatar a taron Kolin, tana kunshe da tsare-tsare masumuhimmancin gaske,to amma ta kasa kaiwa ga sanya tunanin alumomi da mutane da dama su sa zuciya kan Yarjejeniya Ta Duniya.

A dangane da haka ne a shekara ta 1994,Maurice Strong a masayin sa na shugaban Majalisar Duniya,ya hada kai da Milhail Gorbachev wanda ya kasance shugaban kungiyar Green Cross na kasa da kasa,domin su sake kaddamas da sabon shiri na Yarjejeniya Ta Duniya. Jim McNeill,babban sakatarin WCED,da Queen Beatrix da kuma priminsta Ruud Lubbers na kasar Netherlands ne suka hada kai da Strong da Gorbachev. Gwamnatin kasar Netherlands ce ta fara bada taimakon kudi. Shirin tun farko za a tafiyar da shi ne bisa hanyar cimma burin al’umma,domin kuma a zana Yarjejeniya da zai iya bayyana shawarwarin da aka cimma,da al’umomin duniya masu tasowa game da dabi’u,da tsare-tsare game da samar da cigaba mai jurewa nan gaba.

Jakadan kasar Algeria Mohammed Sahnoun shine direkta na farko,kan aikin Yarjejeniya Ta Duniya a shekara ta 1995, yayin da ake cigaba da bada shawarwari da gudanar da bincike a fagen tsarin tafiyar da muhali,da raya kasa mai jurewa, wajen cimma nasarar Doka ta kasa da kasa. An afa sakatariyar Yarjejeniya Ta Duniya a inda Majalisar Duniya take a Costa Rica,karkashin jagorancin babban dirktan majalisar duniya,Maximo kalaw daga kasar Philippines. A shekara ta 1996, Mirian Vilela daga Brazil ta zama shugaba mai tafiyar da ayukan Yarjejeniya Ta Duniye a majalisa Duniya,ya zuwa kashen shekara ta 1996,aka kafa majalisar Yarjejeniya Ta Duniya,domin ta sa ido kan aikin zana shirin. Mirian Vilela tana jagorancin ne tare da Strong da kuma Gorbachev, da kungiyar wasu zababun mutane daga manyan shiyoyin duniya. Majalisar ta gayyaci Steven C. Rockefeller, farfesa a nazarin addini da bin tsari, daga kasa Amirka domin jagoranci da kafa komitin zana shirin Yarjejeniya  na kasa da kasa. Shirin zanen wanda aka fara shi a watan Janeru shekara ta 1997, zai dau tsawon shekaru uku.

Daruruwan kungiyoyi da dubban mutane sun mara baya wajen kirkiro da Yarjejeniya Ta Duniya. An kafa komitoci  arba’in da biyar (45)na kasa da kasa. An gudanar da tattaunaw koina a Duniya da kuma ta duniyar gizo,da manyan tarruruka na shiyoyi da aka yi na Asiya,Afrika,Amirka ta tsakiya da ta kudu,Amirka ta arewa da kuma kasashen Turai. Dukan tunani da shirin Yarjejeniya Ta Duniya suna nuni ne da irin albarkatu na ilimi da na al’umma da ke kunshe ciki, kamar basira na addinan duniya,da manyan al’adu na masana da kuma sabuwar ra’ayi na duniyar kimiya, da sauransu;kamar nazarin muhali da tsirrai da kuma nazarin kimiya game da tarihin duniya da raya kasa. Kamata yayi a dauki Yarjejeniya Ta Duniya a matsayin aikin raya dabi’u na duniya,wadanda ke haifar da batun zattaswar samar da ‘yancin ‘yan adam, ya kuma sami gagarumin goyon baya a shekara ta 1990.

Komitin zana aikin sun udanar da aikin ne kurkusa da kungiyar kare duniya (IUCN) da hukumar raya dokoki kan muhalli tare da sake nazari kan dukan dokoki da aka zattas da yarjejeniyoyi, da kuma na mutane sama da 200. Yarjejeniya Ta Duniya tana gini, da fadada dokokin raya kasa da na muhali a tsakanin kasa da kasa. Takan bayyana tunani da sa zuciya da aka tattauna lokacin tarukan Koli bakwai(7) na majalisar dinkin duniya,a cikin shekara ta 1990 kan muhali,’yancin bil’adam, yawan jama’a,yara,mata,da raya jin dadi, da kuma birni. Tana fahimtar muhimmancin farfado da  aikin sanya kowa cikin tattaunawa irin na demokuradiya domin raya cigaban dan adam,domin kuma a kare muhalli.

Kammalallen aiki da aka yi kan Yarjejeniya Ta Duniya,wanda aka amince da shi a taron majalisar yarjejeniya ta duniya da ya gudana a hedkwatar UNESCO a birnin Paris a watan Maris shekara ta 2000,yana kunshe ne da gabatarwa,manyan manufofi 16,manufofi masu goyon baya 61,da kuma sashen kammala aiki da aka yi mai taken’HANYAR CIGABA’. A gabatarwa an yi nuni ne da cewa mu alumman biladam guda ne, kuma al’umman duniya guda ne da makoma guda. Yarjejeniyar kuwa tana karfafa dukan mutane su fahimmci hakinsu,kowa bisa yadda yanayisa yake da raya jin dadin iyalin duniya baki daya,da kuma na sararraki masu zuwa. Fahimtar dangantakan da ke tsakanin rayuwar biladam da matsalolinsa na muhalli da tattalin arzikinsa,da na ala’dunsa. Yarjejeniya Ta Duniya tana gabatar da tsarin aiki na hadin gwiwa. Taken sassan nan hudu, wadanda aka rarrabe, ya nuna fadin aikin na daya(1) yana girmamawa da kulawa da rayuwan al’umma, na biyu(2) darajar halittu da tsirrai a muhalinsu, na uku(3) cimma gaskiya a fanin tattalin arziki da jin dadin al’umma, na hudu(4) Demokuradiya,ba hatsari, cikin kwanciyar hankali. Yarjejeniya Ta Duniya ta iya gano halay da dabi’u da ake da su tare,don karfafa bada kai game da tsare-tsarenta. Yarjejeniyar na kunshe ne da hangan gaba kan zaman lumana da murnar rayuwa.

II. Shirin Yarjejeniya Ta Duniya Sharata 2000 – 2005

Sashe na biyu na shirin yarjejeniya ta duniya an fara shine da kaddamaswa na musamman da aka yi na yarjejeniya ta duniya a fadar ta da ake kira peace wanda ke Hague a watan Yuni shekara ta 2008. Bayan hakan ya gudana ne, sai hukumar yarjejeniya ta Duniya ta mika hakkin ta na sa ido kan shirin yarjejeniya ta Duniya da kuma na tattalin kudi wa sabon komitin jagoranci da aka kirkiro, wanda ya hada membobi da dama daga hukumar yarjejeniya ta duniya. Hakummar ce ke rike da izini kan yarjejeniya ta Duniya da ke rubuce, membobinta kuwa sun cigaba da bada shawarwari da goyon bayan shirin kowanen su. A shekara ta 2000, an nada Mirian Vilela a matsayin direkta na sakatariyar yarjejeniya ta Duniya a jamai’ar peace. Sama da shekaru biyar da ke gaba ne aka fasara yarjejeniya ta duniyar a harsuna arbain (40), ta kuma sami amicewa daga kungiyoyi sama da dubu biyu da dari biyar, wadanda ke wakiltan ra’ayoyin miliyoyin mutane. Daga cikin kungiyoyin da suka amince da yarjejeniya ta Duniyar sun hada da UNESCO, kungiyar kare doron kasa ta Duniya (IUCN), majalisar kasa da kasa kan kananan shirye – shirye na muhali. (ICLEI), tare ma da taron kansaloli na Amirka. Yarjejeniyar ta Duniyar ta tanada bayanai masu kyau game da muhimman hanyoyin samar da jurariyar hanyar raya kasa da zaman lafirya a duniya, ba tare da bata lokaci ba, tuni har an fara amfani da ita a matsayin kayayakin koyarwa a makarantu, kolejoji da jami’o’i, da shirye shiryen da ba su shafi farin ilimi kai tsaye ba.

An dauki babban mataki wajen ganin yarjejeniya ta Duniyar ta sami karbuwa na musamman, a taron koli na Duniya kan jurariyar raya kasa daya gudana a Johannesburg a shekara ta 2002. A lokacin taron ne shugabanin duniya da na kasashe da dama tare da kungiyoyi masu zaman kansu da suka halarci taron, sun yi jawabai a fili na amincewa da yarjeniyar ta duniyar. Bayyanai na karshe na zattaswan Johannesburg, bai kunshi fayyataccen bayani game da yarjejeniya ta Duniya ba. To amma duk da haka, ya tabbatar da babban take na yarjejeniya ta Duniya, wajen samo kalmomi daga yarjejeniyar wanda ya bayyana cewa “Muna bayyana hakkokin mu ga juna, wa mafi yawan alumma da ke raye, da kuma ga ‘ya’ yanmu”. Kokarin ganin yarjejeniya ta Duniyar ta sami karbuwa gaban babban majalisar Dinkin Duniya na kan cigaba.

Da aka kai shekara ta 2005, An san da yarjejeniya ta Duniyar ne sosai, a duniya, a matsayin bayani game da ma’anar jurewa kalubala da hanga gaba kan jurariyar raya kasa, da kuma ka’idodin tabbatar da raya kasa mai jurewa. An yi amfani da ita a matsayin wata hanyar cimman sasantawa na zaman lumana, a matsayiin kuma takardar sake waiwayawa kan raya cigaba a kasashen duniya bisa bin tsarin aiki, domin kuma zama kayan aiki a hannun gwamnati, domin samar da shugabanci na gari, domin ta zama kayan aikin raya alumomin karkara, da  kuma zama gishiki na gina shirye- shiryen ilimi kan raya kasa mai jurewa. Yarjejeniyar ta kasance da muhimmanci sosai a farin shirin aiwatarwa na shekara goma na majalisar dinkin duniya, kan ilimi domin raya cigaba mai jurewa, sai ECI ta zama abokiyar hulda da UNESCO domin daukaka shirin na shekaru goma.

A shekara ta 2005, komitin jagoranci ta gudanar da muhimman dabaru wajen sake duba hanyoyin cigaba, karfinta da rashin karfin shirin yajejeniya ta Duniya. Wanda ya kunshi tattancewa na ciki da waje. Tantancewa na waje an gudanar da shi ne karkashin Alan Atkisson, wani mai bada shawarwari na kasa da kasa a fanin raya cigaba mai jurewa. Aikin. Bincike da aka yi, ya bayyana cewa an cimma buri sosai daga shekara ta 2000 da 2005, cewa kuma shirin na cike da alkawarai, kuma kamata yayi a cigaba da shi, to amma nasararsa nan gaba ya danganta ne kan sake tsarin gudanarwanta, da kuma shiri na tsawon lokaci muhimmi. Shirin sake duba tsarin aiki wanda aka kamala da taro na musamman na yarjejeniya ta Duniya da ya gudana a Netherlands wanda komitin Dutch na kasar kan hadin kan tsakanin kasa da kasa da raya cigba mai jurewa (NCDO) ta dauki nauyin gudanarwa, wanda ya tara shugabanin da masu kakkarfan ra’ayi na yarjejeniya  ta Duniya sama da 400. A wannan taron ne, aka sanar da shawarar komiti jagoranci na nada Alan Atkisson a matsayin sabon direkto a sakatariyar yarjejeniya ta Duniya.

A lokacin taron Netherlands, kamfanin wallafa takarda na KIT da ke Amsterdam ta fito da wani littafi, wanda Peter Blaze Corcoran, Mirian Vilela da Alide Roerink suka zama Editocin littafi mai taken “yarjejeniya ta Duniya da ke Aiki: wajen cimma burin Duniya mai jurewa”. Wannan littafi da aka wallafa na dauke da rubuce- rubuce sittin, wadanda shugabanin yarjejeniya ta Duniya da magoya bayanta, daga koina a duniya suka yi, ya kuma tanada muhimman bayyanai, game da muhimmanci, yarjejeniya ta Duniya tare da ayukan yarjejeniya ta Duniya.

III. Shirin Yarjejeniya ta Duniya, 2006 Zuwa Yanzu:

A shekara ta 2006 an sake tsarrafa sakatariyar Yarjejeniya Ta Dunuya ya zuwa Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa(ECI). An kafa sabuwar hukuma ta kasa da kasa  kan in da Uku,domin a maye gurbin komitin gudanarwa domin kuma ta sa ido kan manyan shire-shiryen ECI da kananan Ma’aikata. Steven Rockefeller, Razeena Wagiet na Afrika ta kudu da Erna Witoela daga Indonesia, sune aka zaba a matsayin shugabanin sabuwar hukuma ECI da aka kafa. An kuma bude cibiyar sadarwa da muhimman shirye-shirye ta Yarjejeniya Ta Duniya, a Stockholm na kasar Sweden. An sake tsara tsohon sakatariya da Jami’ar Peace zuwa cibiyar Yarjejeniya Ta Duniya kan ilimi domin raya kasa mai jurewa. Hukumar ECI ta rungumi sabbin manufa da sanarwai,ta kuma fara tsarrafa sabbin manufofi da dabaru domin sashe na uku.

Gwamnatoci kasashe sun fara karfafa bada kai na zahiri,kan aikin Yarjejeniya Ta Duniya. Ma’aikatar kula da muhalli ta kasa Brazil ta amince zahiri da sakatariyar ECI da kuma cibiyar kare  hakin dan adam daga Petropolis, wanda Leonardo Boff da Marcia Miranda suka samar domin daukaka Yarjejeniya Ta Duniya zuwa kowane bangare na al’umman kasar Brazil. Lokacin bukin shugaban kasa kan rana ta duniya a shekara ta 2007, Ma’aikatun ilimi da na muhali a gwamnatin kasar Mexico,sun bayyana a fili mika kai da suka yi,wajen yin amfani da Yarjejeniya Ta Duniya cikin munhajan karatu a makarantun kasar ta Mexico. Sauran jihohi da birane da suka amince da yin amfani da Yarjejeniya Ta Duniya ta kuma aiwatar da ita, sun hadu da jihar Queensland,Astireliya, Jamhuriyat Tatarstan,kasar Rasha,da kuma birane kamar  Calgary (Canada), Munich(Jamus) New Dehli(India),Oslo(Norway) da Sao Paulo(Brazil).
A Shekara ta 2006 da 2007, kungiyoyi 4,600 ne suka rattaba hannu suka kuma amince da Yarjejeniya Ta Duniya, duniyar gizo ta Yarjejeniyar,wacce ta fara smun muhimmin cigaba a fanin baki,wanda ya kai har kusan 100,000 a wata. An kaddamas da sabbin shirye-shirye kan addini da kasuwanci. Shirin matasa na Yarjejeniya Ta Duniya ya cigaba da fadada kungiyoyi a sama da kasashe Ashirin da uku(23), Yawan abokan hulda na Yarjejeniye Ta Duniya ya karu zuwa casa’in da bakwai(97) a kasashe hamsin da takwas(58).Yarjejeniyar ta fara daukan wani sabon mataki muhimmi game da batutuwa da suka shafi manufofi kamar yadda matsaloli kamar na canji da ake fuskanta na yanayi ya kara bayyana irin dogara da muke yi kan juna, da kuma bukatar daukan mataki tare.  An gayyaci ECI zuwa wani taro na kasa da kasa kan cudanyan al’adu da addinai wajen cimma zaman lafiya  da shugaban majalisar dinkin duniya ya shirya.

Sakamakon wani taron karawa juna sani na kwanaki uku, game da samar da shirye-shirye na tsawon lokaci,wanda Osca Motomura ya jagoranta a Amnakey a Sao Paulo na kasar Brazil a shekara ta 2007, majalisar ECI ta kaddamas da sabon hanyar rage cinkoso wuri daya na  karfafa arziki don samar da cigaba,wanda aka tsara domin ya kara yawan hadin kai kan shirin ba tare da bukatar sake fadada gudanarwa na tsakiya ba. An billoda sabbin matakai domin samr da tsarin aiki, da hanyoyin tafiyarwa, bisa ayukan rage cinkoso wuri guda domin girmama Yarjejeniya Ta Duniya tare da aiwatar da shirinta.

Bayan shekaru biyu da ake kokarin sauyawa zuwa sashe na uku kan shirin Yarjejeniya Ta Duniya, Alan Atkisson ya sauka daga mukaminsa na babban direkta na ECI a karshen shekara ta 2007, domin ya bada kai sosai kan aikinsa na bada shawarwari, da ayuka makamantan haka. Ya kuma cigaba da zama mai bada shawara ga ECI. Sai Mirian Vilela ta zama babban direkta na ECI da aka zaba,an sake sanya hedkwatar sakatariya ta ECI  a Jami’ar Peace a Costa Rica,tare da cibiyar Yarjejeniya Ta Duniya kan ilimi don raya cigaba. A shekara ta 2007, Erna Witoela ya sauka daga mukaninsa na daya daga cikin shugabanin, sai aka zabi Brenya Mackey ya maye gurbinsa.

Idan aka hangi gaba sai a tarar Yarjejeniyar ta cigaba da girma a matsayin kasa da kasa,tana karfafa yin aiki,tana zama tsarin ilimi da na karamar Doka,da zama abin tuntuba na raya manufofi,tsara dokoki, da kafa matsayi na kasa da kasa da Yarjejeniyoyi. Amincewa da Yarjejeniya Ta Duniya ta zama wata hanyar da ke karfafa cudanya da aikin, tare da yin amfani da Yarjejeniyar a matsayin ma’auni. Hana cinkoso wuri guda na karfafa arziki ya samar da hanyar fadada ayukan Yarjejeniyar a duniya baki daya. Don cimma wannan buri ne kuwa,Majalisar ECI a taron watan Mayu shekara ta 2008, an amince da shirin na tsawon lokaci wanda ya kai ga karfafa hukumomin tabbatar da doka guda shidda(6), wadannan za su billo da sabbin ayuka, masu goyon bayan Yarjejeniya Ta Duniya a fanonin kasuwanci,ilimi,kafofin watsa labarai,addinai,Majalisar dinkin duniya da matasa.