1987 |
Majalisar dinkin duniya karkashin fanin muhali da raya kasa(Bruntland commission) ta bada shawarar a zattas da wata doka kan kare muhalli da raya kasa mai jurewa,a matsayin wata sabuwar yarjejeniya wacce zata zana manya manufofi game da raya kasa. |
1992 |
A taron koli na duniya da ya gudana a Rio de janiero,an taru ne da niyar samar da Yarjejeniya Ta Duniya karbabbiya a duniya baki daya.To amma gwamnatoci sun kasa cimma yarjejeniya kan batun,sai aka amince da zattaswar doka ta Rio kan muhalli da raya kasa a maimakon Yarjejeniyar. |
|
Karkashin jagorancin Maurice Strong,babban sakatarin taron koli na duniya na Rio,aka kafa majalisar Duniya domin karfafa aiwatar da shawarwari da aka amince da su a taron kolin,domin kuma ta yi gwagwarmaya wajen kafa majalisu na kasa domin raya kasa. |
1994 |
Maurice Strong,shugaban majalisar Duniya,da Mikhail Gorbachev,shugaban kungiyar Green Cross na kasa da kasa, suka kaddamas da rubutacen bayyanai na al’umma game da Yarjejeniya Ta Duniya.Gwamnatin dutch ce ta fara bada goyon baya na kudi kan batun. |
1995 |
Majalisar duniya da kungiyar Green Cross na kasa da kasa,sun fara neman shawarwari daga kasashen duniya,da niyyar raya cigaba kan batun Yarjejeniya Ta Duniya,shine ma masana tsakanin kasa da kasa da jamian gwamnatoci suka taru a wani taron karawa juna san game da Yarajejeniya Ta Duniya a Hague. Majalisar Duniya ce ta kafa sakatariya ta kasa da kasa na burin Yarjejeniya Ta Duniyar. |
1996 |
An cigaba da neman shawarwari game da Yarjejeniya Ta Duniya,domin dandalin Rio+5. An shirya takaitattun bayanai da bincike kan manufofin doka ta kasa da kasa da ke da muhimmanci da Yarjejeniya Ta Duniya.A karshen shekarar ne Yarjejeniya Ta Duniya da kungiyar Green Cross na kasa da kasa suka kafa wata hukuma mai zaman kanta ta Yarjejeniya Ta Duniya,domin jagoran aikin tsarrafa Yarjejeniya Ta Duniya,sai aka kafa komitin yin hakan. |
1997 |
Majalisar Yarjejeniya Ta Duniya ta gudanar da taronta na farko a dandalin Rio+5, a kasar Rio de Janeiro. An kuma billo da rubutaccen shawara game da yadda yarjejeniyar zata kasance. A karshen taron ne aka gabatar da ita a matsayin bayanai wadanda ake cigaba da aiki a kai. Ana cigaba da karfafa nema da shawarwari a duniya baki daya. |
1998 |
kungiyoyi daban-daban sun hada kai da tsarin Yarjejeniya Ta Duniya,sun kuma kafa komitoci na Yarjejeniyar a sama da kasashe 35. Wadannan kungiyoyi da wasu da dama, suna bada shawarwari kan samfurin Yarjejeniyar, wanda kae kuma amfani da shi a fagen ilimi. |
1999 |
An fito da samfurin Yarjejeniya Ta Duniya a watan Afrilu, an kuma cigaba da bada shawarwari. Komitoci na kasa da kasa kan Yarjejeniya Ta Duniya sun karu ya zuwa 45. |
2000 |
A watan Maris ne, hukumar Yarjejeniya Ta Duniya ta gudanar da taro a birnin Paris na kasar Faransa domin amincewa kan kammala fitowa da aikin,a matakin karshe. Kaddamas da Yarjejeniyar da aka yi a fili,ya gudana ne a watan Yuni, a fadar Peace da ke Hague. An kafa komitin tafiyar da aiki na Yarjejeniya Ta Duniya domin sa ido kan kashi na gaba. Manyan manufofinsu sune, su karfafa yadda labarai, amincewa, su kuma karfafa aiwatar da Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin al’umomi,’yan kasuwa da gwamnati; su kuma karfafa goyon bayan amfani da Yarjejeniyar a makarantu,Jami’o’I da makamantan su. |
2002 |
Shirin Yarjejenoya Ta Duniya ya yi kokari na musamman wajen samar da amncewa wa Yarjejeniya Ta Duniya a taron Koli na duniya kan raya cigaba da ya gudana a Johnnesburg. Lokacin taron ne kasashe duniya da dama, da kuma kungiyoyi da bana gwamnati ba, suka amince suka kuma nuna goyon bayansu kan Yarjejeniya Ta Duniya,amma dai ba a kammala yin hakan gaban majalisar Dinkin Duniya ba tukuna. |
2005 |
A wannan lokaci an fasara Yarjejeniya Ta Duniya a harsuna talati da biyu,wadanda aka yayata a wurare daban-daban a duniya,kungiyoyi sama da 2,400 ne, wadanda suka hada da UNESCO,IUCN da ICLEI suka amince da ita. An sake duba aikin shirin Yarjejeniya Ta Duniya ciki da waje,tsakanin shekara ta 2000 da 2005. An yi wani taro na musamman kan Yarjejeniya a Duniya + 5, a Amsterdam a watan Nuwamba. A wannan taron ne aka kammala aikin sake duba shirin Yarjejeniya Ta Duniya na shekaru biyar,an yi murnar kammala shirin,an kuma yi shirye- shirye game da kashi na gaba game da shirin Yarjejeniyar. |
2006 |
An kafa sabuwar majalisar kasa da kasa,game da Yarjejeniya Ta Duniya da membobi Ashirin da Uku,domin ta maye gurbin komitin tafiyar da aiki, ta kuma sa ido kan shirye –shirye da ma’aikata na sakatariya. Majalisar tare da Sakatariyar an sake tsarafa su a matsayin Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa (ECI). |
2008 |
A wannan lokaci an fasara Yarjejeniya Ta Duniya a harsuna Arba’in, kungiyoyi 4,600 ne suka amince da ita,wadanda ko hakan ya bayyana ra’ayoyin miliyoyin mutane. Majalisar ECI ta samar da wani sabon tsari na Yarjejeniya Ta Duniya. An kafa sabbin hukumomin karfafa doka masu zaman kansu, guda shidda(6), domin karfafa shirin hana cinkoso a wuraren kasuwanci,ilimi,kafofin yadda labarai, kungiyoyin addinai, Majalisar Dinkin Duniya da matasa. |