Amincewa da mutane da kungiyoyi suka yi wa yarjejeniya Ta Duniyar, ya nuna ke nan akwai niyyar aiwatar da shirin Yarjejeniyar bisa hanyoyin da suka dace. Amincewan yana nufi har ila yau, bada kai ne ga aiwatar da manufofin yarjejeniyar, da kuma niyyar hada kai da sauran mutane.
Akwai wasu hanyoyi da dama, da wadanda suka amince da Yarjejeniyar za su taimaka wajen daukaka manufar shirin Yarjejeniya Ta Duniya. Misali, wata kungiya zata iya amfani da Yarjejeniyar wajen tsarafa ayukan ta, domin su cimma burin nan na Yarjejeniya Ta Duniya, za su iya amfani da ita a fagen ilimi.
Rattaba hannu ko amincewa da Yarjejeniya ta Duniya abu ne wanda kowace kungiya zata iya yi. Yarjejeniya Ta Duniya ysakanin kasa da kasa na kokarin tabbatar da kungiyoyin da suka amince da Yarjejeniyar,ECI tana kuma tabbatar da cewa yin hakan ya kunshi yarda cewa za a bayyana mai amincewa a fili a matsayin mai amincewa ko rattaba hannu kan Yarjejeniyar.
BAYANAI KAN AMINCEWAR:
Za ka iya amincewa da yarjejeniya Ta Duniya ta yanar gizo ko kuma ka aika mana da bayannan ma na amincewa. Za ka iya amfani da wannan samfurin.
“mu da muka rattaba hannu,mun amince da Yarjejeniya Ta Duniya. Mun rungumi manufofin wannan rabutacen Yarjejeniyar. Muna alkawarin hada kai ne da sauran kungiyoyi na duniya domin samun amintacciya da jurariyar kasa cike da zaman lumana, mu kuma yi aiki don cimma burori da manufofin Yarjejeniya Ta Duniya.
Bugu da kari, ana sa ran mai amincewan zai:
- Daukaka Yarjejeniya Ta Duniya ba ji ba gani, ya kuma bi tsarin gudanarwa da aka bayyana a sashe na vi.
- Ka bada naka gudumawa kan aikin Yarjejeniya Ta Duniya, da kuma wasu ayuka karkashin shirin Yarjejeinyar a hanyar da ta fi dacewa.
- Ka aiwatar da Yarjejeniya Ta Duniya a wurin aikin ka/ki da kuma cikin rayuwarka.