Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Yarjejeniya Ta Duniya da ke Aiki

Shirin Yarjejeniya Ta Duniya – Nijeriya.

 
 
TSARIN GUDANARWA GAME DA FADADA AIKIM YARJEJENIYA TA DUNIYA, TA WURIN HANA CINKOSO

GABATARWA:

Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa(ECI) tana karfafa kowa, ya taimaka wajen cimma manufar shirinta. Ana bukatar cikakken goyon bayan  da hadin kan ka. A wannan fanin, ECI tana kokarin daukak shirin a duniya baki daya, wajen karfafa ayukan da za su hana cinkoso wuri guda, a kuma baiwa mutane, da al’umomi, da kungiyoyi ikon tafiyar da ayuka.

Yayin da ECI ke billo da sabon tsari, ta za kuma cigaba da daukaka Yarjejeniya Ta Duniya, ta muhimman hanyoyi daban-daban,tsakanin kasa da kasa. Tana kuma iya shirya ta kuma tafiyar da dan bangare kawai, a yawan ayuka da ake bukata domin aiwatar da burin Yarjejeniya Ta Duniya.

Manufar wannan tsarin gudanarwan shine domin tabbacin gudanar da cigaba kan hana cinkoson ayukan a madadin Yarjejeniya Ta Dunimaya. Ka yi tunani kan tsarin gudanarwa a  matsayin Na’urorin hada kan ayuka na shirin Yarjejeniya Ta Duniya, yayin da ta ke shirin fadadawa ta hanyar rage cinkoso, wanda ya kunshi aikin miliyoyin mutane a fadin duniya.

Cikkaken aiwatar da mafi yawan manufofin Yarjejeniya Ta Duniya,zata bukaci kokarin gwamnatoci, hukumomi da sauran kungiyoyi. To amma batun bada kai wajen samar da shugabanci da kuma canji a duniya, da goyon bayan da ake bida zai samu ne kawai gun mutane su kansu.

Tsarin gudanarwan, bai kasance kammalalle ba. Majalisar Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa za ta rika sa ido da yin ‘yan gyare-gyare lokaci-lokaci, bisa irin darussa da ake koyarwa game da kokarin aiwatar da Yarjejeniyar a wurare dabam-dabam. Majalisar kuwa tana na’am da duk wani bayyani ko goyon baya da ka ke da shi game da su.

TSARIN GUDANARWA

 1. A fara da Yarjejeniya Ta Duniya:- ka bar Yarjejeniya Ta Duniyar ta kasance muhimmin tsarin da kake da shi wajen tafiyar da shirye-shiryen ka, da ayuka da kake gudarwa domin cimma tabbacin aiki.
 2. Kasance abin koyi:- ka yi kokarin zama abin koyi wajen cusa dabi’un Yarjejeniyar cikin aikin ka na yau da kullum, a gida, wurin aiki da kuma cikin al’umma.
 3. Karfafa kanka:- yi aiki gaba gadi, ka kuma kau da shakkan zaka yi nasara a matsayinka na mutum guda, da kuma cewa ayukan ka za su ingiza na mutane da dama.
 4. Hada ka:- ka hada kai ka kasance da ikon iya canje-canje,wajen gina dangantaka da hadin kai da sauran mutane, ka kuma bidi yin nasara, da samar da hanyoyin yin nasara.
 5. Karfafa wasu:- rarraba aiki, don baiwa kowa daman iya magance matsaloli, daukan shawarwari, da jagoranci, da gudanar da ayukan taimakon al’umma.
 6. Inganta halin daraja juna da ganewa:- a tabbatar da gina dangantaka, da daraja juna, daga kungiyoyi ko al’umomi da al’adu dabam-dabam. A kuma iya sasanta rigingimu ta hanyar tattaunawa, don kawo cigaba.
 7. Ka dukufa wajen shirye-shiryenka:- ka dukufa wajen bayyana shirin ka karkashin Yarjejeniya Ta Duniya, ba tare da ka jagorance su ba. Domin su cimma burin kaiwa  ga kungiyoyin al’umma, har ga cimma nasara.
 8. Bada karfi kan ababan da suka haddasa:- ka bada karfi da tunani kan manyan dalilan da suke janyo matsaloli da kalubalai da ke fuskantar biladam, kada kuma ka bar ayuka da ke janyo rashin cigaba, ya dauke hankalin ka daga aikin.
 9. Ka bada kai, ka kuma saki jiki:- kada ka gaza kan batun mika kai,game da manyan manufofi, ka kuma tabbata cewa matakai da za ka dauka suna dai-dai da manufar Yarjejeniya Ta Duniyaa, amma ka saki jiki,inda akwaihanyoyin cimma nasara hakan na dabam.
 10. Ka kasance da basira wajen samar da hanyan aiki:- kada ka kyale hakalinka da aikinka ya kasance kan neman kudi ba, ka yi amfani da tunaninka domin ka kasance da basira wajen samar da hanyar aiwatar da aik.
 11. Yi amfani da kimiya ciki azanci:- ka fahimci cewa mafi yawan mutane ba su da damar kaiwa ga samun kayayyakin kimiya da suka cigaba. Yayin da kuma za ka yi amfani da kimiya wajen magance matsaloli,ka tabbatar ya kasance dai-dai.
 12. Ka kare darajar Yarjejeniya:- yayin gabatarwa, ko samun bayyane daga ciki,ko fasarar yarjejeniya Ta Duniyar, ka tabbatar da aminci wajen amfani da kalmomin da ke cikin rubutu na ainihi, ka kuma gama Yarjejeniyar da kungiyoyi kawai,ayuka da ke tafiya dai-dai da dabi’u da manufa.