Burin Yarjejeniya Ta Duniya (Earth Charter Initiative):
Burin Yarjejeniya Ta Duniya aikine da ya kunshi mutane da dama a bangarori daban-daban na duniya,kungiyoyi tare da kafofi da suka cusa kai wajen karfafa aiwatar da manufofi da dabi’u na wannan Yarjejeniya Ta Duniya.
Burin wannan aikin mai fadi ne,wanda kungiyoyin bada kai da na al’umma suka yi.kungiyoyin sun hada da na kasa da kasa,na gwamnatocin kasashe da hukumominsu, kungiyoyin jami’o’I,kungiyoyi masu zaman kansu da na al’umma,gwamnatin gari, kungiyoyin addinai,makarantu da wuraren kasuwanci da kuma dubban mutane daban-daban.
Mafi yawa daga cikin kungiyoyin sun riga sun amince da Yarjejeniya Ta Duniyar kuma suna amfani da ita wajen karfafa manufofinta, da dama daga cikin kuwa suna amfani da yarjejeniyar ne ba tare da wata kwakkwara izini ba.
Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa (Earth Charter International)
Wannan Earth Charter International (E C I) ta kunshi majalisa da sakatariya. Ta kuma kasance ne domin ta karfafa cigaban burin Yarjejeniya Ta Duniya tare da manufanta. Tana kuma karfafa watsa labarai game da shirin,ta karba ta kuma yi amfani da shi. Tana goyon bayan girma da inganta burin Yarjejeniya Ta Duniya.
An kafa ita wannan E C I a shekara ta 2006 domin a sake tsarrafa a kuma sake fadada ayukan Yarjejeniya Ta Duniya.
Kamata yayi a fahimci cewa,ko da yake majalisar E C I tana shugabncin da ya shafi burin gudanar da aikin baki daya,har yanzu ba ta da ikon shugabancin burin Yarjejeniya Ta Duniya ita kanta. Majalisar na da hakin kuwa ne kawai da E C I .
Hukumar kula da Yarjejeniya Ta Duniya:
An kafa hukumar kula da Yarjejeniya Ta Duniyar ne a farkon shekara ta 1997, a matsayin kungiya na kasa da kasa mai zaman kanta, wanda majalisar duniya da wata kungiyar Green cross ta kasa da kasa suke sa ido kansa, suke kuma bada shawarwari,tare da amincewa da Yarjejeniya Ta Duniyar wadda aka kadamas a shekara ta 2000. Hukumar na da iko kan rubutaccen Yarjejeniya Ta Duniyar, membobinta kuma suna bada shawarwari wa E C I, Jakadu ne kuma na rubutaccan Yarjejeniya Ta Duniyar.
To amma a halin yanzu hukumar bata sa ido kan ayukan burin Yarjejeniya Ta Duniya. An baiwa majalisar E C I hakin yin hakan yanzu.
Majalisar E C I na da hakin sa ido ne kan ayukan Sakatariya ta ECI. Tana kafa manyan manufofi,bukatu da hanyoyin kaiwa ga cimma buri ga majalisar.Tana kuma jagora da shugabancin burin baki daya. Ita majalisar bata sami izinin kasancewa kungiya mai zaman kanta ba. Majalisar tana zaban membobinta ne tare da shawara da kuma goyon bayan sauran membobi a duniya baki daya.
Sakatariya ta ECI
Sakatariyar ECI,wace ke Jami’ar PEACE na kasar Costa Rica, ta dukufa wajen karfafa kudurori,manufofi da bayyanai da majalisar ECI ta runguma. Tana goyon bayan aikin majalisar tana kuma taimakawa da shirye-shirye na musamman,tana kuma daukan nauyin gudanar da yawancin ayukan Yarjejeniyar. Sakatariyar tana jagoranci da hadin kai da kuma niyyar ganin an billo da Yarjejeniyar a fagen ilimi,matasa,wuraren kasuwancin da na addini ta kuma karfafa sadarwa da dukan bangarorin Yarjejeniyar a ko’ina,ta kuma karfafa amfani da Yarjejeniyar a matsayin karamar doka.
Kungiyoyin hadin kai
Kungiyoyi masu hadinkai da ECI,mutane ne daban-daban da kuma kungiyoyi da suka amince da burin Yarjejeniyar,kuma suna mika kai domin daukaka ta. Suna kuma taimakawa wajen aiwatar da manufofin ECI a kasashen su. Kungiyoyin hadin gwiwa sukan shiga wami Yarjejeniya ne na musamman tare da ECI domin su kasance wuraren samun bayyanai mai karfi wa Yarjejeniyar Ta Duniya a kasashensu. Sakatariyar ECI ce ke jagorancin ayukan kungiyoyin khadinkan,ta tanada kayan aiki. Za a iya samun kungiyar hadin kai fiye da daya a kasa guda. Kungiyoyin sun amince su rika sadarwa da Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa(ECI) ta kuma tanada rahotannigame da muhimman ayuka da suka shafi Yarjejeniy Ta Duniyar a yankunan su. ECI ta amince ta rika fadakar da kungiyoyin hadinkan game da manyan shawarwari da kuma ayuka da suka shafe su,ta kuma tanada masu hanyoyin tafyarwa, shawarwarida sadarwa (wanda ke dogara kan tanadin kayan aiki).
Abokan hulda
Abokan hulda na musamman, kungiyoyi ne da ayukan su da kuma shirin su ke goyon bayan Yarjeeniya Ta Duniya da kuma burinta, ko kuma wadanda ayukan su ke dai-dai da manufofin Yarjejeniyar. Yawancin su kuwa kungiyoyin ne na kasa da kasa,za su iya kasancewa na kasashe har ma da matakin yankunan karkara. Abokan hulda kamar haka sukan shiga wata yarjejeniya ce ta musamman,da zai bayyana yadda abokin hulda zai yi aiki wajen mara baya da kuma daukaka Yarjejeniya Ta Duniya da kuma amincewa da su don samun goyon bayan ECI.
Masu rattaba hannu
Mai rattaba hannu zai iya kasancewa mutum guda ko kungiyar da ta amince,ta goyi baya,ta kuma bada kai bisa manufofin Yarjejeniya Ta Duniya. Wannan matsayi kuwa abude yake wa kowace kungiya,komin yawanta da kuma mutane. Sakatariyar ECI ta sami rattaba hanayen manyan-manyan kungiyoyi na kasa da kasa da na kasashe.
Masu bada shawarwari
Masu bada shawarwari na ECI, mutane ne sanannu kuma kwararru a fanin bada shawarwari,masu goyon bayan majalisa da sakatariya ta ECI. Ana gayyatan mutane su bada kai wajen bada shawarwari,bisa irin goyon bayan da suke bayarwa ga Yarjjeniya Ta Duniya, da kuma sanin hanyoyin bada shawarwari da goyon bayawa maalisar ECI,Sakatariya da dukan inda ake bukatan hakan. Babban direkta a Sakatariyar ne ke daukan masu bada shawarwari kan aikin.
Hukumar karfafa doka
An shirya hukumar karfafa dokar ce domin ta yi aiki a matsayin kungiya mai mika kai,wamda zai kai ga cimma burorin masu zaman kansu. Hukumar karfafa doka zata bada karfi kan raya kungiyoyi da ke ko’ina,ta kuma daukaka ayuka a wuraren kasuwanci,ilimi,kafofin watsa labarai,addinai,majalisar dinkin duniya da matasa. Manyan yan majalisar ECI ne zasu amince da aikin shugabancin ayarin kowace hukumaar karfafa doka. Membobin majalisar za su iya kasancewa a hukumar,tare da mutane daban-daban, kungiyoyi abokan hulda,na hadin kai ko masu bada shawarwari. Majalisar ECI ce zata rika duba ko ta sa ido kan cigaban aiki a dukan hukumomin karfafa doka, amma Majalisar ECI da Sakatariya,ba za su jagoranci ayukan hukumar kai tsaye ba.
Masu mika kai/goyon baya
Masu mika kai ko goyon baya,suna matsayin masu rattaba hannu ne,wadanda suka dukufa suka kuma bada agajin lokaci,kudade,hadin kai,inganta dangantaka tsakanin jama’a,ta kowace hanyar da ta cancanta game da Yarjejeniya Ta Duniya a garesu. Za su iya kasancewa kungiyoyi gwamnatoci da na al’umma daban-daban masu mika kai,dai-dai suke da kungoyoyi masu zaman kansu,wadanda ba na gwamnati ba. Basu kuma da cikakken ‘yanci ko hakki bisa aikin goyon baya da suke yi.